Zabura 111 (SRK)
Zabura 111111 Wannan Zabura waƙa ce, layinta sun fara da jerin harufan Ibraniyanci bi da bi.
1Yabi Ubangiji.111.1 Da Ibraniyanci Hallelu Ya
Zan ɗaukaka Ubangiji da dukan zuciyata
a cikin majalisar masu aikata gaskiya da kuma a cikin taro.
2Ayyukan Ubangiji da girma suke;
dukan waɗanda suke farin ciki da su suna tunaninsu.
3Ayyukansa masu ɗaukaka da kuma daraja ne,
adalcinsa kuma zai dawwama har abada.
4Ya sa a tuna da abubuwa masu banmamaki nasa;
Ubangiji mai alheri ne mai tausayi kuma.
5Yana ba da abinci ga waɗanda suke tsoronsa;
yakan tuna da alkawarinsa har abada.
6Ya nuna wa mutanensa ikon ayyukansa,
yana ba su ƙasashen waɗansu al’ummai.
7Ayyukan hannuwansa masu aminci ne da kuma gaskiya;
dukan farillansa abin dogara ne.
8Tsayayyu ne har abada abadin,
ana yinsu cikin aminci da kuma gaskiya.
9Yana ba da ceto ga mutanensa;
ya kafa alkawarinsa har abada,
tsarki da banrazana ne sunansa.
10Tsoron Ubangiji ne mafarin hikima;
dukan waɗanda suke bin farillansa suna da ganewa mai kyau.
Gare shi ne madawwamin yabo.